An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 10 April 2016 04:34

Jami'an Tsaron Labanon Gano Wata Cibiyar 'Yan Ta'adda Mai Hatsarin Gaske A Kasar

Jami'an Tsaron Labanon Gano Wata Cibiyar 'Yan Ta'adda Mai Hatsarin Gaske A Kasar
Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun sami nasarar ganowa da kuma cafke 'yan wata kungiyar 'yan ta'adda mai hatsarin gaske a kasar.

Tashar talabijin din Al-Manar ta kasar Labanon din ta jiyo wata majiyar tsaron kasar tana cewa a baya-bayan nan jami'an tsaron kasar sun gano wata kungiyar 'yan ta'adda da suke gudanar da ayyukan janyo hankulan matasa zuwa ga ayyukan ta'addanci da tura su zuwa kasashen waje don aikata ayyukan ta'addanci.

Rahotannin sun ce ita dai wannan kungiyar tana gudanar da ayyukan nata ne karkashin wata makaranta ta addini da ta bude a daya daga cikin yankunan arewacin kasar, inda babban aikin da suka sa a gaba shi ne shirya 'yan ta'adda.

Rahotannin sun kara da cewa tuni jami'an tsaron suka kama mutane biyar daga cikin 'yan kungiyar wadanda tun da jimawa suke tara matasa da ba su darasin 'jihadi' inda bayan ba su horo sukan tura wasu daga cikinsu zuwa kasar Siriya don shiga kungiyar Da'esh wasu kuma a bar su a cikin kasar ta Labanon don ayyukan ta'addanci.

Majiyar tsaron dai ta ce sanannen dan ta'addan nan da ke garin Riqqa na kasar Siriya Umar al-Satim shi ne yake jagorantar wannan makarantar daga can.

Add comment


Security code
Refresh