An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 09 April 2016 17:03

Koriya Ta Arewa Ta Sake Nasarar Gwajin Makami Mai Linzami

Koriya Ta Arewa Ta Sake Nasarar Gwajin Makami Mai Linzami
Kasar Korea ta Arewa ta sanar Yau Asabar da cewa tayi nasarar sake harba wasu makamai masu linzami samfurin ICMB masu iya kaiwa ko'ina.

Wannan babban ci gaba, a cewar shugaban kasar Koriya ta Arewar Kim Jong-un ya tabbatar da cewa makamin nukiliyar zai iya cimma har Amurka, kmar yadda kanfanin dilancin labaren kasar na KCNA ya rawaito.

Gwajin wannan makamin na yau na nuna cewa kasar Koreya ta Arewa na shirye domin mayar da martani a duk lokacin da ta fuskanci wata barazana daga abokan gaba ta.

Rahotanni na nuna shugaban kasar Kim Jong-Un da kansa ya shugabanci bikin tare da bada umurnin cilla makaman na yau.

Al'amura na dai kara dangulewa ne a wannan yakin tun bayan da koriya ta Arewa ta yi gwajin harba makaman masu linzali a farkon wannan shekara, wanda ya sa kwamitin tsaro na MDD kara kakaba mata takunkumai masu tsauri.

Add comment


Security code
Refresh