An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 09 April 2016 16:22

Afghanistan: Kerry Ya Kira 'Yan Taliban Shiga Shirin Zaman Lafiya

Afghanistan: Kerry Ya Kira 'Yan Taliban Shiga Shirin Zaman Lafiya
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kery ya yi kira ga 'yan Taliban na Afganistan da su shiga shirin samar da zamen lafiya domin kawo karshen zubar da jini a wannan kasa.

Mr Kery ya bayana hakan ne a wani taron manema labarai tare da Shugaban kasar ta Afganistan Ashraf Ghani a yayin wata ziyara ba zata daya kai Kaboul a wannan Asabar.

A yayin ziyara dai bangarorin biyu sun tattauna akan hanyoyin da suke ganin zasu kai ga samun tattaunawar zamen lafiya da 'yan Taliban.

Mahukuntan Kaboul da abokan huldar su Amurka, Sin, da Pakistan sun jima dai suna neman hayoyin tattaunawa ta kai tsaye da 'yan Taliban, saidai har kayo yanzu 'yan taliban din suna akan matsayar su ta kin shiga tattaunawar muddin dai ba'a amunce da bukatar su ba ta neman sojojin kasa da kasa su fice daga Afganistan.

Add comment


Security code
Refresh