An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 09 April 2016 15:41

Amurka Ta Yi Gargadi Akan Yiwuwar Kai Hari A Turkiyya

Amurka Ta Yi Gargadi Akan Yiwuwar Kai Hari A Turkiyya
Ofishin Jakadancin Amurka a Turkiyya ya yi gargadi akan yiwuwar kai hare-hare ta'adanci a biranen Satambul da Antaliya.

Wata sanarwa da offishin ya fitar a shafin sa na internet ya ce akwai yiwuwar kai hare hare a wuraren yawan bude ido na Satambul da kuma Antaliya dake kudancin kasar ta Turkiyya.

Sanarwar ta kuma gargadin 'yan kasar ta Amurka dasu kaurewa wuraren da ake fuskantar cinkoson jama'a da kuma wuraren yawan bude ido.

Dama kafin hakan Isra'la ta fitar irin wannan sanarwa inda ta umurci 'yan kasar ta dasu fice da gaggawa daga kasar Turkiyya saboda barazana kai hare-haren ta'adanci.

A baya bayan nan dai Kasar Turkiyya na fuskantar hare-haren ta'adanci da ake dangantawa da na kungiyar (IS) da kuma wata kungiyar maita suna (TAK) data balle daga kungiyar Kurdawa ta (PKK).

Add comment


Security code
Refresh