An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 09 April 2016 15:15

Djibouti : 'Yan Adawa Sun Kalubalanci Zaben Omar Guelleh

Djibouti : 'Yan Adawa Sun Kalubalanci Zaben Omar Guelleh
'Yan adawa a Djibouti sun kalubanci zaben shugaban kasar da Ismail Omar Guelleh ya lashe da gagarimin rinjaye.

Shugaban kasar Ismail Omar Guelleh , wanda yake shugabancin kasar tun shekara ta 1999 ya sake lashe zaben kasar da aka gudanar jiya Juma’a, a karo na hudu jere da kashi 86.68% na yawan kuriu da aka jefa, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.

'yan adawa dai na cewa anyi arangizon kuri'u, sanan an hana dayewa daga cikin wakilan shiga runfunan zabe.

Dama kafin hakan wasu daga cikin jam'iyyun adawa sun kauracewa zaben.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi shugaban kasar da tauye 'yan cin jama'a.

Add comment


Security code
Refresh