An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 09 April 2016 09:54

Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Yi Gargadi Kan Tabarbarewar Tsaro A Burundi

Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Yi Gargadi Kan Tabarbarewar Tsaro A Burundi
Kungiyoyin kasa da kasa da suke gabatar da tallafin bil-Adama da suka hada da kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross da na Red Crescent sun yi gargadi kan karin tabarbarewan al'amura da zasu wurga jama'a cikin mummunan yana yi a kasar Burundi.

Wakilin kungiyoyin kasa da kasa masu bada agajin gaggawa ta Red Cross da na Red Crescent a kasar Burundi Andrus Sundin ya bayyana cewa; Dubban daruruwan mutane suna cikin halin kaka-ni ka yi sakamakon matsaloli da suka hada da rashin tsaro saboda rikicin siyasa, bullar masifar ambaliyar ruwa, durkushewar harkar tattalin arziki musamman kasuwanci da sauransu, don haka suna bukatar tallafin gaggawa.

 

Andrus ya kiyasta cewa ana bukatar kudade akalla dalar Amurka miliyan daya da dubu dari shida domin tallafa wa jama'a a fuskar tsugunar da su a wajaje masu aminci, samar da kayayyakin kiwon lafiya da bukatun yau da kullum musamman abinci ga mutane akalla 100,000.

 

Jami'in kungiyoyin kasa da kasar ya kuma fayyace cewa: A halin yanzu haka an samu bullar cututtuka a tsakanin 'yan Burundi da tashe-tashen hankula suka raba su da muhallinsu inda suke gudun hijira a wasu yankunan kasar da misalin cutar zazzabin cizon soro da amai da gudawa.

Add comment


Security code
Refresh