An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 09 April 2016 04:04

An Sake Zaben Isma'il Omar Guelleh A Matsayin Shugaban Jibouti

An Sake Zaben Isma'il Omar Guelleh A Matsayin Shugaban Jibouti
Rahotanni daga kasar Jibouti sun ce shugaban kasar Isma'il Omar Guelleh shi ne ya sake lashe zaben shugaban kasar.

A wata sanarwa da Firaministan kasar ta Jibouti Abdulkadir Kamal Muhmamd ya bayar ya sheda cewa, shugaba Isma'il Omar Guelleh ne ya sake lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar, a wani sabon wa'adin mulki na shekaru 5.

 

Guelleh ya lashe zaben da babban rinjaye, bayan da mafi yawan jam'iyyun adawa akasar suka kaurace ma zaben.

 

Tun a cikin shekara ta 1999 ce dai Isma'il Omar Guelleh yake kan kujerar shugabancin kasar Jibouti, kuma a cikin shekara ta 2010 ya yi wa kundin tsarin mulkin kasar garanbawul, inda ya sauya dokar da ta kayyade shugabancin kasar a cikin shekaru 10 kawai a wa'adin mulki guda biyu.

Add comment


Security code
Refresh