An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 17:26

Jami'an Tsaron Belgium Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Harin Ta'addancin Brussels

Jami'an Tsaron Belgium Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Harin Ta'addancin Brussels
Babban mai shigar da kara a kasar Belgium ya sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame wasu mutane da ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai birnin Brussels a kwanakin baya.

Jaridar La Figaro ta kasar Faransa ta buga labarin cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'a, babban mai shigar da karar ya bayyana cewar jami'an tsaron sun sami nasarar kame wasu mutane da ake zargi da hannu cikin harin ta'ddancin da akakai filin jirgin sama da kuma tashar jiragen kasa na birnin Brussels a ranar 22 ga watan Maris din da ya gabata, sai dai kuma sanarwar ba ta yi karin haske kan adadi da kuma sunayen mutanen ba; sai dai kawai ta ce a nan gaba za a yi karin bayani kan hakan.

To sai dai wata majiyar ‘yan sandan ta ce daga cikin wadanda aka cafke din har Mohammed Abrini daya daga cikin wadanda ake zargi da harin ta’addanci da aka kai birin Paris na kasar Faransa da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 130.

A ranar 22 ga watan Maris din da ya gabata ne dai wasu 'yan ta'adda suka kai hari birnin na Brussels lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 35 da kuma raunata wasu da dama.

Add comment


Security code
Refresh