An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 17:16

Firayi Ministan Kasar Madagascar Yayi Murabus Daga Mukaminsa

Firayi Ministan Kasar Madagascar Yayi Murabus Daga Mukaminsa
Rahotanni daga kasar Madagascar sun bayyana cewar firayi ministan kasar Jean Ravelonarivo ya sanar da murabus dinsa daga matsayin bugu da kari kan rusa gwamnatinsa biyo bayan tsanantar takaddamar da ke tsakaninsa da shugaban kasar Hery Rajaonarimampianina.

Rahotannin sun ce bayan makonni na rikici tsakanin firayi ministan da shugaban kasar, a yau firayi ministan ya mika wa shugaban kasar takardar murabus dinsa daga mukamin firayi ministan da kuma rusa gwamnatinsa, lamarin da shugaban kasar ya amince da shi.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar Madagascar ta fitar a yau din ta ce shugaba Hery Rajaonarimampianina ya amince da murabus din firayi minista Jean Ravelonarivo.

Masana dai suna ganin murabus din firayi ministan zai kara kururuta rikicin siyasar da kasar Madagascar take ciki na tsawon shekaru tun bayan da aka hambarar da gwamnarin Marc Ravalomanana a 2009 .

Add comment


Security code
Refresh