An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 17:01

An Hallaka Da Kuma Kama Wasu Sojojin Saudiyya A Kasar Yemen

An Hallaka Da Kuma Kama Wasu Sojojin Saudiyya A Kasar  Yemen
Rahotanni daga kasar Yemen sun bayyana cewar sojojin kasar Yemen da dakarun sa kai na kasar sun sami nasarar hallaka wani adadi na sojojin Saudiyya da kawayenta bugu da kari kan wadanda aka kama a matsayin fursunonin yaki.

Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da sojojin Saudiyyan da kawayenta da suke samun goyon bayan Amurka suka yi shirin kai wani hari a lardin Marib da ke arewacin kasar Yemen din a yau din nan Juma'a inda sojoji da dakarun sa kai na Yemen din suka musu kwanton bauta da kashe wasu daga cikinsu baya ga wadanda kuma suka kama a matsayin fursunonin yaki.

Tashar talabijin din Al-Manar ta kasar Labanon ta jiyo wata majiyar sojin kasar Yemen din tana cewa sojojin sun sami nasarar kama wasu sojojin da suka kai harin wanda Saudiyya da kawayen nata suka fara kai shi tun daren jiya Alhamis har zuwa safiyar yau din nan Juma'a.

Haka nan kuma rahotannin sun ce baya ga sojojin Saudiyya da kawayen nata da aka hallaka da kuma wadanda aka kama, har ila yau sojojin kasar ta Yemen sun sami nasarar tarwatsa wasu motoci da makaman yaki baya ga wadanda kuma suka kwace a matsayin ganima.

Add comment


Security code
Refresh