An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 10:06

An fara gudanar da zaben Shugaban kasar A Djbouti

An fara gudanar da zaben Shugaban kasar A Djbouti
Yau juma’a ana gudanar da zaben shugaban kasa a Djbouti, inda shugaban kasar mai ci Isma’il Umar Guelleh ke fatan samun galaba a wannan zabe.

An dai bude rumfunarn zabe 455 ne domin bai wa mutanen kasar dubu 187 damar jefa kuri’a a wannan karamar kasa mai mutane dubu 800.

'Yan takarkari shida ne dai zasu fafata a wannan zaben da ake gani shugaba Guelleh ne zai sake lashewa a wani wa’adi na hudu, lura da cewa tun da ya dare kujerar milkin kasar babu alamar sauka.

tun daga shekarar 1999 ne Shugaba Ismail Omar Guelleh ke kan karagar milkin kasar kuma daga shekarar 1977 zuwa yanzu dankin Isma'il ne ke rike da madafun iko na wannan karamar kasar da Faransa ta yi mata milkin mallaka.

A shekarar 2010 ne Shugaba Ismail Omar Guelleh ya yiwa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima inda aka cire dokar da kayyada wa'adin milki daga cikin kundin tsarin milkin kasar.

Add comment


Security code
Refresh