An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 09:45

Amincewar Banki Duniya wajen bayar da Bashi ga Kasar Tanzania

Amincewar Banki Duniya wajen bayar da Bashi ga Kasar Tanzania
Banki Duniya ya amince Baiwa Kasar Tanzaniya Bashin Dalar Amurka million 65

A jiya Alkhamis , Babban Darakten Bankin kasar Tanzania Bella Bird ya bayyana cewa Bankin Duniya ta amince da Baiwa kasar bashin dalar Amurka million 65, kuma Gwamnati za ta yi amfani da wadannan kudade wajen karfafa matakan tsaro da kuma ci gaban 'yan kasar domin tabbatar da adalci a tsakanin Al'ummar kasar

Rahoton ya ce an bayar da wannan bashi ne domin shirin aikace aikace na bunkasa kasar zuwa shekarar 2025, kuma Gwamnatin ta Tanzania na da shirin samar da aiyukan yi da kuma samar da guraren aiyukan yi ga Matasa kafin karshen wannan shekara.

Rahiton ya ce a 'yan shekarun nan , tattalin arzikin kasar na karuwa ta yadda idanuwan kasashen Duniya suka mayar da hankali ga kasar, an ce a ko wata shekara tattalin arzikin kasar ke karuwa da kashi 7%, amma har yanzu kasar na fama da talauci.

Add comment


Security code
Refresh