An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 08:55

Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane 2 a kasar Somaliya

Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane 2 a kasar Somaliya
Akalla Mutane biyu ne suka sara rayukansu sakamakon buda wuta da wasu 'yan bindiga suka yi a birnin Magadushu fadar milkin kasar Somaliya.

Shaidu da ido a birnin na Magadushu sun shaidawa manema labarai cewa Wasu 'yan bindiga ne da ba a kai ga gane ko su waye ba suka buda wuta daidai lokcin almuru na jiya Alkhamis kusa da fadar Shugaban kasar dake yankin Banadir, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 tare da jikkata wasu 13 na daban.

Muhamad Usaman kwamishinan yankin na Banadir ya tabbatar da wannan Labari, inda ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkatan zuwa Asibiti kuma wasu daga cikinsu na cikin halin mutu kwakai rai kwakwai.domin haka a kwai yiyuwar adadin mutanan da suka rasa rayukan su ya karu nan gaba.

Duk da cewa babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, saidai Kwamishin yankin na Banadir ya dora alhakin harin kan kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab.

Kungiyar ta Ashabab na amfani da raunin Gwamnatin ta Somaliya wajen fadada kai hare-haren ta a cikin kasar.

Add comment


Security code
Refresh