An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 04:37

Fira Ministan Kasar Senegal Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar Mauritaniya

Fira Ministan Kasar Senegal Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar Mauritaniya
Fira ministan gwamnatin kasar Mali ya isa birnin Nouwakshot fadar mulkin kasar Mauritaniya da tawagar da ke rufa masa baya da nufin tattauna hanyoyin bunkasa alaka da huddar tattalin arzikin kasashen biyu.

A jiya Alhamis ne fira ministan kasar ta Senegal Muhammad Ben Abdullahi Dionne da tawagar da ke rufa masa baya suka isa kasar ta Mauritaniya domin gudanar da ziyarar aiki na kwanaki biyu da nufin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

 

Daga cikin tawagar fira ministan kasar ta Senegal akwai ministan makamashi Thierno Al-Hasan Sall da ministan sufuri Mansur El-Yamen Kan. Senegal da Mauritaniya dai kasashe ne da suke da makobtaka da juna, kuma suna da alaka mai kyau a tsakaninsu don haka suke neman bunkasa alakar musamman a fuskokin daban daban da nufin habaka ci gaban kasashensu.

Add comment


Security code
Refresh