An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 08 April 2016 04:00

Ana Ci Gaba Da Samun Marayu A Palasdinu Musamman A Yankin Zirin Gaza

Ana Ci Gaba Da Samun Marayu A Palasdinu Musamman A Yankin Zirin Gaza
Kididdiga ta tabbatar da cewa; A halin yanzu haka akwai kananan yara marayu da yawansu ya doshi dubu ashirin 22 da suke rayuwa a yankin Zirin Gaza, kuma kungiyar daya ce kacal mai suna "Amal" ke tallafa musu.

Kafar watsa labaran Pars Today ta kasar Iran ta watsa rahoton cewa; Sakamakon ci gaba da killace yankin Zirin Gaza da ake yi, hakan ya janyo tabarbarewan harkokin tattalin arziki a yankin lamarin da ya shafi cibiyar ta "Amala" kai tsaye, don haka cibiyar bata samun ci gaba da ayyukanta kamar yadda suka dace.

Babban daraktan gudanarwa ta Cibiyar ta "Amal" Ayad Al-Misri ya bayyana cewa; Mafi yawan marayun a yankin Zirin Gaza sun rasa mahaifan sune sakamakon hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take kai wa kan yankin, kuma a halin yanzu yankin yana fuskantar matsalar karancin kayayyakin aiki a fuskar kiwon lafiya.

Add comment


Security code
Refresh