An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 07 April 2016 18:12

'Yan Adawa Mauritania Suna Bukaci Wasu Ministoci Da Su Yi Murabus

'Yan Adawa Mauritania Suna Bukaci Wasu Ministoci Da Su Yi Murabus
'Yan adawa akasar Mauritania sun bukaci wasu daga cikin ministocin da suke mara baya ga shugaban kasar da su yi murabus.

Shafin yada labarai na Afrik Time ya bayar da rahoton cewa, jagoran kawancen jam'iyyun adawa na kasar Saleh Wuld Hanana shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce suka kira da babbar murya ga ministocin da suke mara baya ido rufe ga shugaban kasar Muhammad Wuld Abdulaziz da su yi murabus ba tare da wani bata lokaci ba, domin kuwa a cewarsa su ne ummul haba'isin duk wata barna akasar.

Gwamnatin kasar Mauritania dai ta kirayi dukkanin bangarorin adawa zuwa zaman tattaunawa, domin samo zaren bakin warware matsaloli da dama da ke tsakaninsu, amma da dama daga cikinsu sun yi watsi da wannan goron gayyata.

Add comment


Security code
Refresh