Print this page
Thursday, 07 April 2016 18:02

Riek zai Koma Juba Domin Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa

Riek zai Koma Juba Domin Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa
Madugun 'yan tawayen kasar Sudan ta kudu Dr. Riek Machar ya ce zai koma birnin Juba fadar mulkin kasar domin kafa gwamnatin rikon kwarya kuma ta hadin kan kasa.

Machar ya bayyana ranar 18 ga wannan wata na Afirilu a matsayin ranar da zai isa Juba, inda zai hadu da shugaban kasar Salva Kiir, kuma za su jagoranci kafa gwamnatin rikon kwarya wadda za ta hada dukkanin bangarori a kasar.

Tun a cikin shekara ta 2013 ce dai shugaba Salva Kiir ya safke Riek Machar daga mukaminsa na mataimakin shugaban kasa, tun daga lokacin kuma suka fara takun saka, inda gwamnatin kasar ta dare biyu, wasu na goyon bayan shugaban kasar, wasu kuma suna goyon bayan Riek Machzr, inda daga karshe dai ya shelanta tawaye, kuma manyan janar-janar na sojin kasar suka mara masa.

Daga karshe dai bisa matsin lambar majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyi na kasa da kasa, bangarorin biyu sun amince su kafa gwamnatin hadin kasa ta rikon kwarya.

Related items

Add comment


Security code
Refresh