An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 07 April 2016 16:47

A Yau Yahudawan Sahyuniya Sun Afka Kan Makabartar Annabi Yusuf (AS) A Nablus

A Yau Yahudawan Sahyuniya Sun Afka Kan Makabartar Annabi Yusuf (AS) A Nablus
yahudawan sahyuniya sun afka kan makabartar annabi Yusuf (AS) da ke birnin Nablus a gabar yamma da kogin Jodan.

Tashar talabijin ta Palastine Today ta bayar da rahoton cewa, kimanin yahudawan sahyuniya 1000 ne da jijjifin safiyar Alhamis suka shiga cikin makabartar, ayyin da motocin jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila suke yi musu rakiya tare da ba su kariya.

Dukkanin yahudawan da suka shiga wannan wuri mai tsarki dai mazauna wasu matsugunnai ne da aka gina a kusa da birnin na nablus.

Yahudawan sun bayyana cewa suna gudanar da taronsu ne na Tilmudi da suke yi shekara-shekara, kuma a wanann karon a kabarin annabi Yusuf za su gudanar da shi.

Daruruwan matasan palastinawa sun fito domin kin amincewa da wannan mataki na yahudawan sahyuniya, da suke shirin gudanar da taronsu kan kabarin annabi Yusuf (AS), amma jami'an yan sandan Isra'ila sun yi amfani da kulake da hayaki mai sanya hawaye domin tarwatsa matasan palastinawa.

Haka nan kuma rahoton ya kara da cewa a jijjifin safiyar yau jami'an tsaron haramtacciyar kasar Israila sun kame wasu mata biyu, bayan da suka kai farmakia gidansu kimanin karfe 4 na safe, inda suka kame Dalal Al-haslamun yar sheakara 47 da kuma Aidah Saidawi, inda aka yi awon gaba da su, da ba a san inda aka kai su ba.

Add comment


Security code
Refresh