An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 07 April 2016 05:39

Aljeriya Ta Ja Kunnan Faransa Kan Badakallar Panama

Aljeriya Ta Ja Kunnan Faransa Kan Badakallar Panama
Ma'aitakar harkokin wajen kasar Aljeriya ta kirayi jakadan kasar Faransa domin nuna masa rashin jin dadin ta dangane da yadda kafofin yada labaren Faransan sukayi ta sukan shugaba Buteflika akan balakalar kaucewa biyan haraji ta Panama Papers.

A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ta fitar ta ce jaridun Faransa sun wuce gona da iri akan wannan batu, bisa fakewa da cewa icin fadar albarkacin baki.

wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wannan shekara da ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ke kiran jakadan Faransa.

Ministan harkokin wajen kasar ta Aljeriya Ramtane Lamamra ya nemi ga hukumomin Faransa dasu yi allawadai da wannan sokana dake zama babban kalubale ga huldar diflomatsiya dake tsakanin kasashen biyu.

A fitowar ta baya bayan nan jaridar ''le Monde'' ta kasar Faransa ta zayyano sunayen wasu mayan jami'ai da shugabanin duniya a cikin ciki harda shugaba Abdel Azizi Bouteflika a cikin badakalar nan ta kaucewa biyan haraji da halasta kudaden haramun da ake kira da ''Panama Papers''.

Add comment


Security code
Refresh