An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 07 April 2016 04:31

Libya : Khalifa Ghweil, Ya Ce Ba Zai fice Daga Tripoli Ba

Libya : Khalifa Ghweil, Ya Ce Ba Zai fice Daga Tripoli Ba
Shugaban gwamnatin birnin Tripoli da duniya bata amunce da ita ba, ya ce shi fa ba zai fice ba daga birnin ba, kwana guda bayan sanarwar da da mambobin gwamnatin sa suka fitar na goyan bayan gwamnatin hadin kan kasa dake samun goyan bayan MDD.

A wata sanarwa daya sanya ma hannu ya kuma wallafa a shafin gwamnatinsa Khalifa Ghweil ya yi kira ga ministocin sa da kada su fice daga gwamnatin, tare da yin barazana daukan mataki kan duk wanda ya shiga gwamnatin ta hadaka da Fayez al-Sarraj ke jagoranta.

A ranar Talata data gabata wata sanarwa da ma'aikatar shari'a Libya ta fitar ta sanar da kawo karshen aikin gwamnatin ta Tripoli da duniya bata amunce da ita ba, a wani mataki na kawo karshen zubar da jini da kaucewa kasar fadawa cikin rudani ko rarabuwa.

A kasa da mako guda da kama aiki gwamnatin hadaka ta Tripoli dake samun goyan bayan MDD ta samu goyan baya daga wasu mahimman bangarori na wannan kasa da suka hada da babban banki, kanfanin mai dama wasu mayan biranen kasar.

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh