An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 17:49

Dauki Ba Dadi A Garin Benghazi Na Kasar Libiya Ya Jikkata Sojojin Gwamnati Da Dama

Dauki Ba Dadi A Garin Benghazi Na Kasar Libiya Ya Jikkata Sojojin Gwamnati Da Dama
Majiyar asibitin Jala'a da ke garin Benghazi na kasar Libiya ta sanar da jikkata sojojin gwamnatin kasar da dama a wani dauki ba dadin da suka da mayakan tsoffin 'yan tawayen kasar a gabashin garin na Benghazi.

Babban jami'in watsa labarai na asibitin Jala'a da ke garin Benghazi na kasar Libiya Fadaya Barghusi ya bayyana cewa; Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin hadin kan kasa da gungun mayakan kungiyoyin tsoffin 'yan tawayen kasar musamman kungiyar Ansarul-Shari'a ya yi sanadiyyar jikkatan mutane da dama ciki har da sojojin gwamnatin Libiya guda takwas.

Wannan gumurzu ya kunno kai ne a daidai lokacin da fira ministan gwamnatin hadin kan kasa Fayez al-Sarraj ya koma birnin Tripoli fadar mulkin kasar da zama a kokarin da yake yi na ganin ya shawo kan tashe-tashen hankula a Libiya.

Add comment


Security code
Refresh