An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 15:31

Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Yi Nasarar Halaka 'Yan Ta'adda Da Dama A Kasar

Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Yi Nasarar Halaka 'Yan Ta'adda Da Dama A Kasar
Sojojin gwamnatin Siriya sun kai wasu jerin hare-hare kan sansanonin 'yan ta'adda a wasu yankunan kasar lamarin da ya janyo halakar 'yan ta'adda da dama tare da tarwatsa motocin yakinsu.

Kamfanin dillacin labaran kasar Siriya ta SANA ya sanar da cewa: A hare-haren da sojojin kasar suka kaddamar kan sansanoni daban daban na 'yan ta'addan kungiyar Da'ish musamman a gefen garin Hamah da yammacin garin Homs da kuma gabashin garin Diri-Zur sun yi nasarar halaka tarin 'yan ta'adda dama tare da jikkata wasu adadi mai yawa.

Har ila yau sojojin na Siriya sun yi nasarar tarwatsa motocin yakin kungiyar ta Da'ish fiye da ashirin a yankin arewa maso gabashin garin Tadmir. A gefe guda kuma kwararru kan harkar lalata bama-bamai 'yan kasar Rasha sun samu nasarar lalata bama-bamai da yawansu ya kai 120 da 'yan ta'adda suka dasa da nufin aiwatar da kisan gilla kan fararen hulan Siriya a garin Boustani na kasar.

Add comment


Security code
Refresh