An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 08:14

Amnesty International ta bayyana damuwarta kan yadda aka yankewa Mutane hukuncin kisa A Saudiya

Amnesty International ta bayyana damuwarta kan yadda aka yankewa Mutane hukuncin kisa A Saudiya
Kungiyar Kare hakin bil-Adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bayyana damuwarta kan yadda aka yankewa Mutane hukuncin kisa A Saudi-arabiya

A wani rahoto da ta fitar jiya, kungiyar Amnesty International ta tabbaya damuwa game da yadda hukunci kisa ya karo a Saudiya, inda ya ce a shekarar da ta gabata an yankewa Mutane 158 hukncin kisa a Kasar, kuma idan aka kwatamta da shekarar 2014,hukuncin ya ninka a shekarar da ta gabata.

Rahoton ya ce a shekarar da ta gabata a yanke hukuncin kisa ga Mutane dubu daya da 624,idan kuma aka kwatamta da shekarar 2014,batun ya karo da kashi 50%.

Masanan harakokin shara'a sun yi imanin cewa kotun Saudiya ba ta gudanar da adalci a yayin yanke hukuncin, saidai tana biyayya ne kawai ga abinda zai farantawa masarautar kasar rai.

A 'yan kwanakin da suka gabata kotun ta Saudiya ta yanke hukuncin bulala dubu daya tare kuma da daurin shekaru 10 ga Za'if Badawi, lamarin da ya sanda masu rashin kare hakin bil-adama a kasar su ja hankalin magabatan kasar da kadda su zartar da wannan hukinci, domin hakan na iya sa ya rasa ransa.

Add comment


Security code
Refresh