An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 07:49

Najeria ta bukaci Gwamnatin Burundi da 'yan Adawa su zauna kan tebirin shawara

Najeria ta bukaci Gwamnatin Burundi da 'yan Adawa su zauna kan tebirin shawara
Gwamnatin Najeria ta bukaci Gwamnatin Burundi da 'yan Adawa su zauna kan tebirin shawara

A yayin ganawar sa da Pierre Buyoya tsohon shugaban kasar Burundi, Shugaba Buhari na Nijeria ya bayyana damuwarsa kan yanayin da kasar Burundi ta shiga tare da bayyana goyon bayansa kan kokarin da kungiyar tarayyar Afirka ke yi da nufin medo da zaman lafiya a kasar ta Burundi.

Shugaba Buhari ya ce wajibi ne Shugaba N'kurinziza na Burundi tare da shugabanin 'yan adawar kasar sun zauna kan tebirin shawara domin kaucewa abin zai biyo baya a nan gaba kuma Gwamnatin Nijeria za ta yi kokarinta domin tabbatuwar hakan.

A nasa Bangare tsohon Shugaban kasar ta Burundi Pierre Buyoya da yanzu hakan yake a matsayin babban jami'in kungiyar Taryyar Afirka ya yi maraba da matakin da Najerian ta dauka.

Rikicin Siyasar kasar Burundin wanda ya samo asali tun bayan da shugaba N'kurinziza ya bayyana aniyarsa ta tazarce a watan Avrilun shekarar bara, ya yi sanadiyar mutauwar mutane 400 yayin da ya raba wasu dubu 240 da mahalinsu.

Add comment


Security code
Refresh