An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 06 April 2016 03:55

'Yan Tawayen Kasar Libya Sun Mika Mulki Ga Sabuwar Gwamnatin Kasar

'Yan Tawayen Kasar Libya Sun Mika Mulki Ga Sabuwar Gwamnatin Kasar
'Yan tawayen Libya dake rike da madafun ikon kasar a birnin Tripoli sun sanar da mika mulki ga sabuwar gwamnatin kasar wacce take samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar 'yan tawayen sun sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar a jiya Talata inda suka ce sun dau wannan matakin ne don share fage ga gwamnatin hadin kan kasar da take samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya gudanar da aikinta da kuma kaucewa zubar da jini a kasar.

Har ila yau 'yan tawayen wadanda suka kafa gwamnatinsu da suka kira ta ceton kasa karkashin jagorancin Khalifa al-Ghawil sannan kuma suke rike da babban birnin kasar Libiyan, Tripoli da wasu yankuna masu yawa na yammacin kasar tun shekara ta 2014, sun ce sun dakatar da dukkanin wani aiki na gwamnatin ta su da kuma dukkanin jami'an gwamnatin.

A ranar Larabar da ta gabata ce sabon firayi ministan gwamnatin hadin kan kasar Libiyan Fayez al-Sarraj da 'yan majalisar ministocinsa suka isa birnin Tripolin don karbar madafan ikon kasar gaba daya, duk kuwa da cewa har ya zuwa yanzu akwai wasu hukumonin a kasar ta Libiya musamman a gabashin kasar wadanda ba su amince da sabuwar gwamnatin ba.

Add comment


Security code
Refresh