An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 05 April 2016 09:08

Dubban mutane sun fara gudu daga gidajensu a birnin Brazaville na kasar Kongo.

Dubban mutane sun fara gudu daga gidajensu a birnin Brazaville na kasar Kongo.
Sakamakon tashin hankali, Dubban mutane sun fara gudu daga gidajensu a birnin Brazaville na kasar Kongo.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa, a jiya Litinin duban mazauna birnin Brazaville na kasar Congo sun fara barin gidajensu sakamakon masayar wutar da ake tsakanin dakarun tsaro da 'yan tawaye.

Wakilin kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP ya shaidar da ganin mazauna yankin na tserewa daga gidajensu cikin yanayi na dimauta, domin neman mafaka a tsakiyar garin.

Wannan rikicin na zuwa ne a daidai lokacin da kotun tsarin mulkin Kasar ke nazarin halarcin sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana ranar 20 ga watan Maris, wanda shugaba mai ci Denis Sassou Nguesso ya lashe, sakamakon da manyan 'yan takara biyar suka yi watsi da shi bisa zargin tabka magudi.

Jami'an Gwamnatin ta Kongo sun bayyana harin a matsayin ta'addanci tare da bayyana cewa za ta gudanar da bincike domin gano ko harin ya nada alaka da kauracewar da 'yan adawar suka yi a zaben shugaban kasar da ya gabata.

Add comment


Security code
Refresh