An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 05 April 2016 03:53

Dakarun Iraki Sun Yi Wa Birnin Falluja Da Ke Hannun ISIS Kawanya

Dakarun Iraki Sun Yi Wa Birnin Falluja Da Ke Hannun ISIS Kawanya
Dakarun kasar Iraki tare da sojojin sa kai na kasar sun yi wa birnin Falluja da ke hannun mayakan 'yan ta'adda na Daesh (ISIS) kawanya.

Tashar talabijin ta Al-Irakiya ta bayar da rahoton cewa, dubban sojojin gwamnatin Iraki ne tare da mayakan sa-kai suka yi wa irnin Falluja kawanya daga bangarori daban-daban, tare da yanke hanyoyin da 'yan ta'addan suke samun dauki daga wasu kasashen larabawa da ke makwaftaka da kasar ta Iraki.

 

Rahoton ya kara da cewa a jiya sojojin an Iraki sun gano wani gatafaran gida a kusa da birnin na Falluja, wandaa cikinsa ake kera bama-bamai da rokoki gami da nakiyoyi, da kuma harhada jigidar bama-bamai da masu kunar bakin wake ke amfani da su wajen tarwatsa kansu, a cikin masallatai ko kasuwanni da dai sauran wuraren hada-hadar jama'a a cikin kasar ta Iraki.

Add comment


Security code
Refresh