An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 05 April 2016 02:49

WHO: Sakamakon Yakin Saudiyya A Yemen Mutane Miliyan 19 Na Bukatar Taimako

WHO: Sakamakon Yakin Saudiyya A Yemen Mutane Miliyan 19 Na Bukatar Taimako
Hukumar lafiya ta duniya ta ce kimanin mutane miliyan 19 daga cikin mutane kimanin miliyan 24 na kasar Yemen suna bukatar taimako, yayin da miliyan 14 kuma suke da bukatar taimako da ya hada har da bangaren kiwon lafiya, sakamakon yakin da Saudyya ta kaddamar kan kasar.

A cikin rahoton da ya gabatar wa majalisar dinkin duniya, babban wakilin hukumar lafiya ta duniya a kasar ta Yemen Ahmad Shadul ya bayyana cewa, yanayin da al'ummar kasar ke ciki ya yi muni matuka, domin kuwa Saudiyya ta rusa rayuwar al'ummar kasar musamamn ta fuskar tattalin arziki da kuma kiwon lafiya, inda ta rusa fiye da kashi 28 na asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na kasar.

A nata bangaren hukumar UNICEF a wani rahoton da ta fitar a makon da ya gabata wanda shi ma ta mika shi ga majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewa kanan yara fiye da 2000 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren Saudiyya a kan kasar Yemen daga watan Maris na 2015 da ta gabata ya zuwa watan Maris na 2016 da muke ciki.

Add comment


Security code
Refresh