An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 04 April 2016 17:42

Amurka Ta Aike Da Wasu Fursunonin Guantanamo Zuwa Kasar Senegal

Amurka Ta Aike Da Wasu Fursunonin Guantanamo Zuwa Kasar Senegal
Ma'aikatar tsaron kasar Amurka, Pentagon, ta sanar da tusa keyar wasu 'yan kasar Libiya su biyu da sojojin Amurkan suke tsare da su a gidan yarin nan na Guantanamo da ke kasar Cuba na tsawon shekaru zuwa kasar Senegal don ci gaba da tsare su a can.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ne ya ba da labarin inda ya ce mutane biyu dai suna daga cikin gungun fursunonin da ake tsare da su a Guantanamon ne da ake sa ran za a rarraba su zuwa alal akalla kasashe biyu da suka amince su karbe su a shirin da gwamnatin Obama ta Amurka take da shi na rufe gidan yarin ihunka banzan da ke ci gaba da zubar da mutumcin Amurka sakamakon irin azabtar da mutanen da ake da tsare da su a wajen ake yi.

Ma'aikatar tsaron Amurkan dai ta sanar da cewa mutane biyun da aka kai su kasar Senegal din su ne Salem Abdu Salam Ghereby da kuma Omar Khalif Muhammad Abu Baker Mahjour Umar dukkanin 'yan kasar Libiya ne.

Rahotanni dai sun ce a halin yanzu dai fursunoni 89 suka rage a gidan yarin na Guantanamo wadanda mafi yawa daga cikinsu ana tsare da su na tsawon shekaru masu yawa ba tare da shari'a ko kuma gurfanar da su a gaban kotu ba lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah daga cibiyoyin kasa da kasa da kungiyoyin kare hakkokin bil'adama.

Add comment


Security code
Refresh