An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 04 April 2016 16:58

Tonon Silili: Wasu Manyan Masu Fadi A Ji A Duniya Ba Sa Biyan Haraji

Tonon Silili: Wasu Manyan Masu Fadi A Ji A Duniya Ba Sa Biyan Haraji
Jami'an gwamnatocin kasashe da 'yan siyasa daban-daban na duniya suna ci gaba da mayar da martani da mafi girman tonon silili da bayyanar da takardun bayanan sirri da ke bayanin yadda wasu wasu attajirai da manyan masu fada aji na duniya ke boye dukiyoyinsu don guje wa haraji.

Kafafen watsa labaran kasashen Yammaci ne suka ba da labarin wannan tonon sililin inda suka sanar da cewa wani kamfanin lauyoyi na kasar Panama da ke gudanar da ayyukansa a asirce ya fitar da wasu takardun kudi na sirri kimanin miliyan 11 da suka alakanta shugabanni da manyan jami'an kasashe 72 na duniya wadanda ke kan mulki a yanzu ko kuma suka sauka da kokarin safarar kudade da kaucewa biyan haraji bugu da kari kan kaucewa takunkumin kasa da kasa.

Rahotannin sun ce daga cikin wadanda aka bayyana cewa suna da hannu ko kuma na kurkusa da su suna da hannu cikin wannan badakalar har da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, firayi ministan Birtaniyya David Cameroon, haka nan da firayi ministocin kasashen Pakistan da Iceland da dai sauransu.

Wasu rahotanni sun ce daga cikin wadanda sunayensu ya bayyana cikin wadannan takardu har da iyalan shugaban majalisar dattawan Nijeriya Bukola Saraki inda aka ce sun boye wasu kadaroria kasashen waje ba tare da sanin hukumomin Nijeriya din ba, lamarin da ake ganin zai kara wa shugaban majalisar damuwar da yake ciki na zargin da ake masa na kin bayyanar da hakikanin kadarorin da ya mallaka kamar yadda doka ta tanadar a kasar.

Tuni dai wasu kasashe da suka hada da Australia, Austria, Brazil, Fransa da Sweden suka fara gudanar da bincike kan wannan lamarin.

Add comment


Security code
Refresh