An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 04 April 2016 10:01

'Yan tawaye sun kai hari kan ofishin 'yan sandar birnin Brazaville na kasar Congo

'Yan tawaye sun kai hari  kan ofishin 'yan sandar birnin Brazaville na kasar Congo
Al'ummar babban birnin Congo sun wayi gari cikin tashin hankali na musayar wuta tsakanin 'yan tawaye da jami'an 'yan sanda

Wani babban jami'in Gwamnati da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaidawa manema Labarai cewa yan tawayen Tinija ne suka kaiwa ofishin 'yan sandar dake anguwar Makélékélé hari, inda aka dinga masayar wuta tun daga daren jiya Lahadi har zuwa wayewar garin yau Litinin.

Mazauna Anguwar ta Makélékélé sun shaida cewa an fara musayar wutar ne tun daga karfe 2:00 agogon kasar wato karfe 3:00 agogon GMT sai zuwa karfe 6:00 na safe abin ya lafa, sannan daga karfe 8:30 na safiyar yau din an ci gaba da jin karar manyan makamai a ariyar gurin. ya zuwa yanzu babu wani cikekken bayyani kan asarar rayuwar da wannan hari ya janyo.

Kungiyar 'yan tawayen ta Tinija na daga cikin kungiyoyi 'yan tawayen da suka yaki gwamnatin Congo a yakin cikin gida na sherara 1998 zuwa 1999, a shekarar 2003 sun cimma yarjejjeniyar sulhu tsakanin su da gwamnati.

Tun bayan da shugaba Denis Sassou N’Guesso ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban kasar 'yan tawayen suka soma kai hare haren kan jami'an gwamnatin kasar.

Add comment


Security code
Refresh