An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 04 April 2016 08:27

Wani Baom ya Tashi a arewacin birnin Bagdaza na Iraki

Wani Baom ya Tashi a arewacin birnin Bagdaza na Iraki
Majiyar labaran Kasar Iraki ta sanar da tashin Bom a Arewacin birnin Bagdaza

Tashar Telbijin din Al'irakiya ta habarta cewa A yau din nan wani Bom ya tashi a kusa da gadar Almussana dake arewacin birnin Bagdaza, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar fararen hula da dama.

A jiya Lahadi ma wani Bom din ya tashin a birnin Bagdazan, inda fararen hula da dama suka jikkata, wasu kuma suka rasa rayukansu.

A yayin da kungiyar 'yan ta'addar Da'esh ko kuma ISiS ke shan kanshi a hanun dakarun tsaron da kuma na sa kai a irakin, yanzu sun koma kai hare-haren kunan bakin wake a cikin manyan buranan kasar iinda suke kashe fararen hula da ba su ji ba su gani ba.

Bisa wani rahoto da tawagar MDD dake kasar Iraki wato Yunami ta fitar, a watan Maris din da ya gabata hare-haren ta'addanci a kasar ya yi sanadiyar mutuwar Mutane dubu daya da 119, sannan wasu dubu daya da 561 suka jikkata.

Add comment


Security code
Refresh