An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 04 April 2016 04:56

Dan Majalisar Dokokin DR Congo Ya Koka Kan Janyewar Sojojin Kasar Daga Yankin Gabashin Kasar

Dan Majalisar Dokokin DR Congo Ya Koka Kan Janyewar Sojojin Kasar Daga Yankin Gabashin Kasar
Dan Majalisar Dokokin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo mai wakiltan lardin Kivu ta Arewa ya koka kan matakin da rundunar sojin kasar ta dauka na janyewa daga yankin Bibua-Ruvungi da ke lardin Kivu ta Arewa.

Juvenal Munubo dan jamalisar dokokin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo mai wakiltan Lardin Kivu ta Arewa ya bayyana tsananin damuwarsa kan matakin da rundunar sojin kasar ta dauka na janyewa daga yankin Bibua-Ruvungi da ke garin Walikale a lardin Kivu ta Arewa.

Juvenal Munubo ya kara da cewa; Janyewar sojojin kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da yankin Bibua-Ruvungi ya wurga al'ummar yankin cikin fargaba da tsoro saboda yiyuwar bullar 'yan tawaye a yankin da zasu zo domin cin zarafin mutane tare da wawushe musu dukiyoyi, don haka ya gabatar da kira ga rundunar sojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da su canja ra'ayi domin masalahar kasa.

Add comment


Security code
Refresh