An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 03 April 2016 17:54

Babban Bakin Libya Da Kanfanin Mai Sun Goyi Bayan Gwamnatin Hadaka

Babban Bakin Libya Da Kanfanin Mai Sun Goyi Bayan Gwamnatin Hadaka
Babban bakin Libya da kanfanin mai na kasar NOC sun sanar da goyan su ga gwamnatin hadaka ta kasar dake samun goyan bayan MDD a karkashin jagorancin Fayez al-Sarraj.

A wata sanarwar daya fitar yau lahadi babban bakin kasar ya ce yana maraba da zuwan gwamnatin tare da yin na'am da kudirin da kwamitin tsaro na MDD ya dauka wanda a cewar sa ita ce hanya daya cilo ta kawo zamen lafiya da hadin kan al'umma wannan kasa.

Wannan na zamen babban ci gaba da zai kara ma gwamnatin samun gindin zama a wannan kasa dake fama da gwamnatoci guda uku.

kazalika hakan zai zama babban kalubale ga wacen gwamnatin Tripoli da kasashen duniya basu amunce da ita ba, dama wace keda mazauni a birnin tobruk dake gabashin kasar .

Har kawo yanzu dai wadanan gwamnatoci guda biyu sun ki amuncewa da gwamnatin hadaka wace ke samun goyan bayan kasashen duniya.

ko a ranar juma'a data gabata kwamitin tsaro na MDD ya nuna goyan bayan ga gwamnatin ta hadaka.

A ranar laraba data gabata ce shugaban gwamnatin hadaka na kasar Fayez al-Sarraj ya samu isa birnin na Tripoli.

Add comment


Security code
Refresh