An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 03 April 2016 17:07

An cafke Jagoran Kungiyar Islama Ta Ansaru A Najeriya

An cafke Jagoran Kungiyar Islama Ta Ansaru A Najeriya
Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cafke jagoran kungiyar islama ta Ansaru dake da alaka da kungiyar 'yan ta'ada Al'Qaida reshen kasashen larabawa ta Aqmi a cikin kasar.

Sanarwar ta ce an cafke Khalid al-Barnawi a ranar Juma'a data gabata a wani samame da jami'am tsaron kasar suka kaddamar a a garin Lokoja na jihar Kogi dake tsakiyar kasar.

wannan dai a cewar kakakin rundinar sojin kasar babban ci gaba a yakin da kasar keyi da ta'adanci.

Rundinar sojin kasar ta ce Khalid al-Barnawi na a sahun gaba a cikin jerin 'yan ta'adan da take nema ruwa a jallo.

ko baya haka al'barnawi na cikin jerin 'yan ta'ada na duniya da Amurka ke nama ruwa a jallo da suka hada da Abubakar Shekau jagoran kungiyar Boko Haram, da Abubakar Adam Kambar wanda ya kirkiro kungiyar Ansaru da kuma Kahalid al barnawi wanda ya dauki jagoranci kungiyar bayan hallaka kambar a wani harin sama da aka kai mabuyar sa a Kano dake arewa Najeriya a watan Maris na shekara 2012

Add comment


Security code
Refresh