An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 03 April 2016 10:02

Dangantaka Na Ci Gaba Da Yin Tsami A Tsakanin Senegal Da Gambia

Dangantaka Na Ci Gaba Da Yin Tsami A Tsakanin Senegal Da Gambia
Ana ci gaba da kai ruwa rana a tsakanin kasar Senegal da kuma makwbciyarta kasar Gambia.

Kamfanin dillancin labaran kasar faransa ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Gambia ta kai Senegal kara ga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS.

Gwamnatin kasar ta Gambia ta zargi Senegal da kokarin yi ma tattalin arzikinta zagon kasa, ta hanyar hana manyan motocin kasarta masu daukar kaya shiga cikin kasar ta Gambia, yayin da kuma kasar Senegal ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon kara kudin haraji da kasar ta Gambia ta yi a kan motocin daukar kayan, amma dai za a warware matsalar ta hanyar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

Add comment


Security code
Refresh