An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 02 April 2016 10:08

Rasha Ta Soki Zama Kan Tsaro Dangane Da Nukiliya A Amurka

Rasha Ta Soki Zama Kan Tsaro Dangane Da Nukiliya A Amurka
Rasha ta yi kakkausar suka dangane da zaman da aka gudanar a kasar Amurka kan batun tsaro da ya shafi nukiliya.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa daga birnin Moscow na kasar Rasha ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey lavrov ya bayyana taron na Amurka da cewa, taro ne da aka gudanar da shi daga bangare guda kawai.

 

Lavrov ya ce Rasha tana girmama ra'ayin kasashen da suka halarci taron, amma ita ta dauki matakin kin halartar wannan taro, saboda babu daidaito a cikinsa, domin kuwa Amurka tana neman ta maye gurbin cibiyoyi na kasa da kasa ne, kamar majalisar dinkin duniya, hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wadanda su ne ya kamata su shirya taron ko kuma ashirya tare da su, amma Amurka ta yi gaban kanta.

 

Kasar Rasha dai ita ce wadda ke yin kusa kunnen doki da Amurka wajen mallakar makaman nukiliya a duniya, kuma ba ta halrci zaman taron ba.

Add comment


Security code
Refresh