An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 01 April 2016 17:42

Kungiyar Boko Haram ta ce za ta ci gaba da gwagwarmaya

Kungiyar Boko Haram ta ce za ta ci gaba da gwagwarmaya
Kungiyar Boko Haram ta ce tana nan daram dakam kuma za ta ci gaba da gwagwarmaya

A wani sabon bidiyo da ta fitar yau a Juma’a, Kungiyar Boko Haram ta karyata mika wuya, kamar yadda ake ikirari bayan fitowar wani faifai bidiyo da ta fitar mako guda da ya gabata , inda aka kwado shugabanta Abubakar Shekau yana gudanar da jawabi cikin yanayin da ya sha bam-bam da yadda ya sa

Bidiyon ya nuna mayakan kungiyar guda 9 dauke da bindiga kirar AK-47 a gaban wata mota kirar Toyota Hilux da wata motar yaki ta soja.

A cikin jawabinsa da ya gabatar da harshen Hausa, daya daga cikin mayakan kungiyar boko haram din yayin da suka rufe fuskokinsu suna sanye da kakin soja yace babu wata tattaunawa tsakaninsu da gwamnati kuma ba batun tsagaita wuta.

Sannan yace za su ci gaba da yaki.Sai dai bidiyon bai nuna fuskar Shugaban mayakan ba Abubakar Shekau daga cikin wadanda suka rufe fuskokinsu.Mai magana a madadin Kungiyar Boko Haram a bidiyon yace har yau har gobe Abubakar Shekau shi ne shugabansu tare da danganta su da mayakan da ke da’awar jihadi a kasashen Iraqi ,Libya da Syria.

Shugaban kungiyar ta Boko Haram ya jima bai fito ba a bidiyon da kungiyar ke fitarwa sai a makon jiya inda ya jinjinawa mayakan kungiyar tare da bayyana cewa su ci gaba da jihadi saboda da .....kuma shi a yanzu saidai abinda ...ya yi.

Add comment


Security code
Refresh