An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 01 April 2016 10:25

Yahudawan Sahyuniya Na Shirin Gina Sabbin Gidaje A Kusa Da Masallacin Quds

Yahudawan Sahyuniya Na Shirin Gina Sabbin Gidaje A Kusa Da Masallacin Quds
Haramtacciyar kasar Isra'ila na shirin gina wasu sabbin matsugunnan yahudawan 'yan kaka gida a yankin Jabal Mukabbir da ke kusa da masallacin Aqsa mai alfarma.

Mai aiko wa tashar talabijin ta Alalam rahotanni daga birnin Quds Khudr Shahin ya bayyan cewa, an gabatar da wannan kudiri ga majalisar ministocin yahudawan kuma ta maince da hakan.

Wannan shiri dai ya hada da gina manyan gine-gine guda 18, wanda za su kunshi gidaje da dama, inda za a tsugunnar da wasu dubban yahudawan 'yan kaka gida, duk kuwa da cewa wannan ya yi hannun riga da yaejejeniyar da aka cimmawa da yahudawan.

Wadannan gine-gine dai za su kunshi gidaje guda 1400, inda kuma za a gina su yanki ne na Palastinawa, wanda Isra'ila ke shirin rusa dukkanin gidajen palastinawa da ke wurin gami da kaddarorinsu.

Khalil Tafkiji wani jami'in Palastinawa mai kula da harkokin tasrin gari da kuma gine-gine ya bayyana cewa, wannan yan adaga cikin shirin da Isra'ila take da shi na mamaye birnin Quds baki daya tare da mayar da shi na yahudawa zalla daga nan zuwa shekara ta 2020, inda za ta gina karin sabbin gidage guda dubu 85 a cikin birnin na Quds, domin tsugunnar da yahudawa a cikinsu.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da suka hada da na majalisar dinkin duniya da na kungiyar tarayyar turai duk sun yi Allawadai da wanann mummunar manufa ta yahudawan Sahyuniya, amma sakamakon goyon bayan da yahudawan da yahudawan sahyuniyan suke sau daga gwamnatin Amurka, yasa suna ci gaba da yin watsi da kiraye-kirayen da duniya ke yi musu.

Add comment


Security code
Refresh