An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 01 April 2016 06:37

An Damu Game Da Zarge-zargen Fyade A Afrika Ta Tsakiya

 An Damu Game Da Zarge-zargen Fyade A Afrika Ta Tsakiya
Babban kwamishinan MDD kan harkokin 'yancin dan adam, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce abun damuwa ne zarge zarge baya bayan nan na fyade da cin zarafin mata da sojojin MDD, Faransa da masu dauke da makamai dake Afrika ta Tsakiya suka aikata.

An samu muhimmin cigaba domin gudanar da bincike kan wadannan zarge zarge da tawagogin ma'aikatan MDD da dama da aka tura a wannan yanki suka gano a 'yan makwanni biyu da suka gabata, in ji mista Zeid, a cewar wata sanawa ta ranar Alhamis.

 

"MDD za ta yi iyakacin kokari domin gudanar da bincike kan wadannan zarge zarge na wuce gona da iri, da suka shafi wasu ayyukan fyade kan mata da 'yan mata masu yawa a wannan kasa.

 

 

Add comment


Security code
Refresh