An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 29 March 2016 04:06

An Tsaurara Matakan Tsaro A Fadar White House Bayan Harbe-Harben Majalisar Dokokin Amurka

An Tsaurara Matakan Tsaro A Fadar White House Bayan Harbe-Harben Majalisar Dokokin Amurka
Rahotanni daga kasar Amurka na nuni da cewa an kara tsaurara matakan tsaro a fadar White House ta shugaban kasar Amurka da hana shiga da fice bayan harbe-harbe da aka yi a wata cibiyar saukar baki a Majalisar Dokokin Amurka, da ake kira da US Capitol.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce jim kadan bayan harbe-harben da aka yi a majalisar dokokin, jami'an tsaron kasar sun rufe fadar ta White House da hana shige da fice don kare lafiyar shugaban kasar da sauran manyan jami'an da suke wajen.

A wata sanarwa da hukumar 'yan sandar kasar Amurkan suka fitar sun ce jami’an tsaro sun sami nasarar kama mutumin da ya bude wuta a cibiyar saukar baki ta Majalisar Dokokin Amurkan bayan an harbe shi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan lamarin, kamar yadda suka ce an jikkita wani dan sanda guda.

Har ya zuwa yanzu dai ba a tantance dalilin da ya sanya mutumin bude wuta din ba.

Add comment


Security code
Refresh