An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 28 March 2016 16:28

Sama da Sojojin Saudiya 100 ne aka kame a yemen

Sama da Sojojin Saudiya 100 ne aka kame a yemen
Dakarun tsaron kasar Yemen da na sa kai sun samu nasarar kame Sojojin haya na Saudiya sama da 100 a yankuna daban daban na kasar

A wani rahoto da ta fitar yau, gidan telbijin din Almasira na kasar yemen ya habarta cewa Dakarun tsaron kasar tare da na sa kai sun samu nasarar kame sama da sojin haya na masaurautar Ali sa'oud 100 a yankunan Marib, Jauf da kuma Baida'a.

A jiya Lahadi, Dakarun tsaron na yemen sun hallaka sojojin hayar saudiya da dama a yayin wani farmaki da suka kai garin Ta'az.

Kungiyar Ansarulla.. ta kasar Yemen ta bayyana masayar fursunan da ta yi tare da kasar Saudiya a matsayin takin farko na girmama Dan Adam a yayin yakin na Yemen.

Bisa yarjejjeniyar da aka cimma kasar Saudiyan za ta saki mayakan kungiyar Ansarulla...100 a madadin sojojin saudiyan guda 9.

Add comment


Security code
Refresh