An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 28 March 2016 09:40

Wani Kwamandan Kungiyar Jihadul-Islami Ta Palasdinu Ya Yi Shahada

Wani Kwamandan Kungiyar Jihadul-Islami Ta Palasdinu Ya Yi Shahada
Wani kwamandan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihadul-Islami a Palasdinu ya yi shahada sakamakon harin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Majiyar kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Jihadul-Islami ta sanar da cewa; Daya daga cikin kwamandojin kungiyar mai suna Muhammad Abid da ake masa lakabi da Abu-Muhammad dan shekaru 47 a duniya ya yi shajhada a yau Litinin bayan fama da jiyya da ya yi sakamakon harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai masa a kwanankin baya.

Jami'in watsa labarai na kungiyar Jihadul-Islami Daud Shahab ya bayyana cewa; Hare-haren wuce gona da irin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna ci gaba da lashe rayukan Palasdinawa, don haka ya zame dole al'ummar Palasdinu su zage dantse a fagen kare kansu daga bakar siyasar zaluncin Yahudawan Sahayoniyya.

Add comment


Security code
Refresh