An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 March 2016 05:32

Obama: Bata Sunan Musulmi Aikin ‘Yan Ta’adda Ne

Obama: Bata Sunan Musulmi Aikin ‘Yan Ta’adda Ne
shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa bata sunan musulmi da musulunci aikin 'yan ta'adda ne kuma su ne hakan yake amfanarwa.

Tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi na mako-mako, Barack Obama ya yi Allawadai da harin da aka kai birnin Brussels na kasar Belgium, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 34 tare da jikkatar wasu kimanin 300, wanda Daesh ta dauki nauyin kai harin.

Obama ya isar da sakon ta’aziyarsa ga iyalan Amurkawa biyu da suka rasa rayukansu a harin, tare da yin fatan samun lafiya ga wasu Amurkawa 14 da suka samu raunuka a harin.

Ya ce ko shakka babu wannan aikin ‘yan ta’adda ne, kuma suna son su tunzura mu ne domin mu dauki matakin takura ma musulmi a kasarmu, ya ce Amurka kasa ce wadda kowa yake da yancin yin addininsa, a kan haka ya ce ‘yan ta’adda ne suke kokarin bata sunan musulmi da ayyukansu na ta’addanci.

Furucin an Obama dai ya zo a matsayin mayar damartani ga Donal Trump dan takatar shugabancin Amurka, wanda yake kokarin tunzura Amurka kan musulmi bayan kai harin na Brussels.

Add comment


Security code
Refresh