An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 27 March 2016 04:44

Sabon Shugaban Kasar Benin Zai Rage Yawan Shekarun Shugabancin Kasar

Sabon Shugaban Kasar Benin Zai Rage Yawan Shekarun Shugabancin Kasar
Zababben shugaban kasar Benin ya sanar da cewa daga cikin abubuwan da zai aiwatar har da rage yawan shekarun wa'adin shugabanci a kasar.

Zababben shugaban na Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya bayyana cewa, a ganinsa shekaru biyar sun yi yawa ga wa'adi guda na shugabancin kasa, a kan hakan zai bukaci a yi gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar domin canja wannan doka, wadda za ta bayar da damar rage yawan shekarun shugabancin kasar.

Haka nan kuma ya bayyana cewa zai rage yawan ministocin kasar daga 28 zuwa 16, domin yin tattali a kan kudaden da gwamnatin kasar take kashewa ga ma'aikatu.

Add comment


Security code
Refresh