An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 26 March 2016 16:19

Congo : An Kirayi Jama'a Da Su Kalubalanci Zaben Nguesso

Congo : An Kirayi Jama'a Da Su Kalubalanci Zaben Nguesso
'Yan takara hudu a zaben shugaban kasar Congo sun yi kira ga daukacin al'umma kasar dasu kalubalanci zaben da shugaban kasar Denis Sassou Nguesso ya lashe tun zagayen farko.

Wata sanarwa da 'yan takaran da suka sha kaye a zaben suka sama hannu tayi kira ga al'umma kasar dasu kalubalanci zaben na ranar 20 ga watan Maris cikin lumana, inda kuma suke kira ga al'ummar dasu tsaya gidajen su a ranar Talata nan mai zuwa 29 ga wata.

idan ana tune Mr Nguesso ya lashe zaben da sama da kashi 60% na kuri'un da aka kada, al'amarin da 'yan takara suka ce tamakar ya kwashi garabasa ne.

'yan takara dai sun zasu ci gaba da kalubalantar zaben ta hanyoyin yajin aiki, gangami, zanga-zanga ta lumana har sai an yi gyara ga haramtacen zaben.

'yan takara sun hada Guy-Brice daya zo matsayi na biyu a zaben da kashi 15% da janar Jean-Marie Michel Mokoko daya zo na uku da kusan kashi 14% da Claudine Munari da kuma Andre Okombi Salissa.

Add comment


Security code
Refresh