An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 26 March 2016 09:28

Sojojin H.K.Isra'ila Sun Jikkata Palasdinawa Akalla 6 A Yankuna Daban Daban Na Palasdinu

Sojojin H.K.Isra'ila Sun Jikkata Palasdinawa Akalla 6 A Yankuna Daban Daban Na Palasdinu
Sojojin gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai farmaki kan yankunan Palasdinawa daban daban lamarin da ya janyo dauki ba dadi tsakaninsu da matasan Palasdinawa a jiya Juma'a.

Kakakin ma'aikatar lafiya ta Palasdinawa a yau Asabar ya sanar da cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai samame a yankin garin Baitu-Hanun da ke arewacin Zirin Gaza lamarin da ya janyo dauki ba dadi tsakaninsu da matasan Palasdinawa, inda sojojin suka bude wutan bindiga da haka ya kai ga jikkatan wasu matasa biyu.

Har ila yau sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila sun jikkata wasu Palasdinawa biyu a yankin gabashin Zirin Gaza ta hanyar harbinsu da bindiga, kamar yadda wani bapalasdine ya jikkata sakamakon fesa masa iskar gas mai guba da sojojin haramtaciyar kasar ta Isra'ila suka yi a yankin sansanin 'yan gudun hijira ta Al-Buraij da ke Zirin Gaza.

Add comment


Security code
Refresh