An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 26 March 2016 04:43

'Yan gudun Hijra Da Dama Sun shiga mawuyacin halin bayan da kasar Girka ta rufe iyakokinta

'Yan gudun Hijra Da Dama Sun shiga mawuyacin halin bayan da kasar Girka ta rufe iyakokinta
Dariruwan 'Yan gudun hijra ne ke mawuyacin hali a kasar Girkai sakamakon rufe iyakokin Balkan da Makduniya

Kamfanin dillancin labaran Faransa Press ya habarta cewa dariruwan 'yan gudun hijra ne ke jibke cikin mawuyacin hali a tsibirin Piraeus dake jihar Attic na kasar Girka, inda suke jan dogon layi domin karbar taimakon abinci da ruwan sha daga ma'aikatan Agaji na Majalisar dinkin Duniya.

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Girka da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaida cewa daga ranar 4 ga watan Avrilu mai kamawa a su fara mayar da 'yan gudun hijrar siriyan zuwa kasar Turkiya.

A nasa bangare Alexis Tsipras Piraministan kasar Girka ya tabbatar da cewa ba za su budewa 'yan gudun hijrar iyakokin su ba, domin haka ne ma ya bukaci 'yan gudun hijrar dake jibke a wannan kasa da kadda su jefa rayuwarsu cikin hadari, su gaggauta rubuta sunayansu a sansanin 'yan gudun hijrar dake yankuna daban daban na cikin kasar domin a mayar kasar Turkiya.

kwanaki 13 da kasar ta Girka ta rufe iyakokin Balkan da a Maknudier, lamarin da ya yi sanadiyar dakatar da duban 'yan gudun hijra a tsibirin Aydumi, inda yanzu haka a kwai 'yan gudun hijra kimanin dubu 12 dake jibke a wannan yanki ba tare da sanin makomarsu ba.

Add comment


Security code
Refresh