An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 26 March 2016 03:45

Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da kisan kwamanda na biyu cikin kungiyar ISIS

Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da kisan kwamanda  na biyu cikin kungiyar ISIS
A wani taron manema labarai da ta kira jiya Juma'a, Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da hallaka 'yan ta'addar ISIS da dama daga cikin su har da kwamanda na biyu cikin kungiyar

Kamfanin dillancin Labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Janar Joseph Dunford shugaban Rundunar hadin gwiwa na kasar Amurka na cewa Magabatan Washinton na da tabbacin cewa an hallaka Abdurraham Mustapha Qaduli kwamanda na biyu a kungiyar ISIS sakamakon hare-haren jiragen yakin Amurka da suke kaiwa maboyar 'yan ta'addar ISIS din a kasar Siriya

Abdur Rahman Mustafa al-Qaduli ya kasance cikin 'yan gaba-gaba da sashin shari'a na kasar Amirka ke nema ruwa a jallo.Babban kwamanda na biyu a rundunar mayakan IS ya hallaka ne cikin wannan wata, kamar yadda ma'aikatar tsaron ta Amurka ta sanar. Shashin shari'a dai na kasar Amirka tun da fari ya bayyana cewa zai bada lada na dala miliyan bakwai ga duk wanda ya bada bayanai da suka kai ga kama wannan jigo na kungiyar ta IS.

Add comment


Security code
Refresh