An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 25 March 2016 17:06

Wata 'Yar Kunar Bakin Wake A Kamaru Da Ta Ce Tana Cikin 'Yan Matan Chibok

Wata 'Yar Kunar Bakin Wake A Kamaru Da Ta Ce Tana Cikin 'Yan Matan Chibok
Jami'an tsaron kasar Kamaru sun ce a yau Juma'a sun kame wata 'yar kunar bakin wake da take shirin tayar da bam, wadda ta ce tana cikin 'yan matan sakandare na Chibok da 'yan Boko Haram suka sace.

Bayanin ya ce an kame 'yan matan su biyu suna dauke da jigidar bama-bamai da suke shirin tarwatsa kansu a yau Juma'a a wani yanki na arewacin kasar ta Kamaru, inda daya ta ce tana cikin 'yan matan Chibok.

Jami'an sojojin an kasar Kamaru sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin, musamman ma dai kan furucin da daya daga cikin 'yan matan biyu ta yi da ke cewa tana cikin 'yan matan sakadandaren Chibok, ta hanyar yin aiki na hadin gwiwa tare da sojojin najeriya kan wannn lamari, domin kuwa Najeriya na da jerin sunaye da hotunan dukkanin 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace a cikin watan Afirilun shekara ta 2014.

Add comment


Security code
Refresh